Goyon bayan gwamnatin kasar Afghanistan da Amurka ke yi ya ba ta damar sanarwa jiya Laraba cewa ba za ta halarci taron wasu kasashe a watan gobe a kasar Rasha wanda zai tattauna akan makomar Afghanistan din.
Yayin da kungiyar ‘yan ta’adan Taliban ta tabbatar wa Muryar Amurka cewa ta amince da goron gayyatar da aka ba ta kuma ta ce za ta tura wakilanta a wurin taron.
Rasha, ko baya ga gayyatar gwamnatin Afghanistan da kuma ‘yan Taliban, haka kuma ta gayyaci wasu kasashe 11 dake yankin kasar, ciki ko har da China,Pakistan da Iran domin su halarci wannan taron 4 ga watan Satumba da za a yi a fadar gwamnatin Rasha.
Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Afghanistan din Sibghatullah Ahmadi ya tabbatar wa Muryar Amurka a ranar Laraba cewa gwamnati ta yanke shawarar kin aikewa da wakilinta wajen wannan taron da za ayi a Rasha, sai dai bai ba da ko wane irin dalili ba.
Rahotanni sun bayyana cewa kasar ta Afghanistan ta yi fushi da matakin da Rasha ta dauka na gayyatar ‘yan Taliban ba tare da tuntubar ita gwamnatin ta Afghanistan ba.
Wannan ne dai karo na farko a cikin shekaru da yawa da kungiyar Taliban za ta halarci irin wannan tattaunawar a hukumance, wanda kuma wannan zai zame wani baban nasara ga harkokin diflomasiyyar kasar ta Rasha.