‘Yan wasan Najeriya na Super Eagles sun nuna jimaminsu ga wadanda suka rasa rayukansu a lokacin da Najeriya take karawa da ‘yan wasan Afirka ta Kudu a wasan dab da na karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON.
Rahotanni da dama daga Najeriya sun ruwaito mutuwar akalla mutum biyar yayin da aka yi fafatawar mai zafi wacce ta ta da hankulan masu kallo musamman lokacin da aka shiga zangon bugun fenariti.
Wasan wanda aka buga a ranar Laraba a birnin Bourke na kasar Ivory Coast ya kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da aka tashi da ci 1-1 duk da karin lokaci da aka yi.
A karshe Najeriya ta doke Afirka ta Kudu da ci 4-2 a bugun na fenariti. Wannan nasara ta ba ‘yan wasan na Super Eagles damar zuwa wasan karshe a gasar.
Najeriya za ta hadu da Ivory Coast mai masaukin baki a wasan karshe a ranar Lahadi.
Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ne ya jagoranci tawagar ‘yan wasa na Najeriya yayin nuna zaman nuna jimamin inda aka yi tsit na dan wani lokaci don yi wa mamatan addu’a.
"In Allah ya yarda, za mu daga wannan kofi a ranar Lahadi wanda za mu sadaukar ga wadanda suka mutu." In ji Musa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ga wasu daga cikin ‘yan Najeriya wadanda suka rasa rayukansu a lokacin wasan kamar yadda jaridun Najeriya suka ruwaito:
- Mai kula da sha’anin kudi na Jami’ar Jihar Kwara, Alhaji Ayuba Abdullahi
- Tsohon dan majalisar wakilai kuma jigo a jami’yyar APC mai mulki, Dr. Cairo Ojougboh
- Dan kasuwa/Dan Najeriya mazaunin Ivory Coast, Chief Osondu Nwoye
- Mazaunin jihar Ogun, Mikail Osundiji
- Mai aikin bautar kasa a jihar Adamawa, Samuel (babu cikakken bayani kan sunan mahaifinsa)