Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Za Ta Kara Da Ivory Coast A Wasan Karshe Na Gasar AFCON


Ivory Coast AFCON Soccer
Ivory Coast AFCON Soccer

Najeriya za ta kara da Kwaddebuwa a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka a ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairun da mu ke ciki bayan kasashen biyu su ka yi nasara a wasan kusa da karshe na gasar da suka fafata yau, Laraba, 7 ga watan Fabrairu.

Najeriya ta fitar da Afirka ta Kudu a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta bugun fenariti da ci 4-2 bayan an tashi wasa ci 1-1.

Williams Troost-Ekong ne ya zura wa Najeriya ta bugun fenariti a minti na 67 kafin Afirka ta Kudu ita ma farke ta bugun fenariti saura minti uku a tashi wasa.

Bayan an tashi wasan 1-1, sai aka kara minti 30 inda cikinta ba a samu wanda ya yi nasara ba.

Cikin fenariti biyar Najeriya ta shigar da guda 4, ita kuma Afirka ta Kudu ta shigar da guda biyu inda kasashen biyu suka barar da dai dai.

A dayan wasan tsakanin masaukin baki Kwaddebuwa ta ci DR Congo 1-0 wadda ya tabbatar da hayewanta zuwa wasan karshe.

Sebastian Haller ne ya zura wa masaukin bakin a minti na 65 da buga wasa.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG