AFCON: Egypt, Senegal Sun Kai Zagayen Semi-Finals

'Yan wasan Egypt suna murnar lashe wasansu a gasra AFCON

Yanzu Egypt za ta kara da Kamaru wacce tuni ta shiga zagayen semi-finals bayan doke Gambia, Senegal kuma za ta kara da Burkina Faso.

‘Yan wasan kasar Egypt sun kada takwarorinsu na Morocco gida bayan da suka doke su a zagayen quarter-finals a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake yi a Kamaru.

Egypt ta doke Morocco ne da ci 2-1.

Dan wasan Morocco Sofiane Boufal ne ya fara zura kwallo a minti na shida da bugun fenariti bayan da aka kwade Achraf Hashimi.

Mohamed Salah ya farke kwallon a minti na 53 bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Wasan dai ya yi zafi bayan da aka yi kunnen doki tsakanin kasashen biyu, wadanda dadaddun abokanan hamayya ne a fagen kwallon kafa.

Kwallo ta biyu ta zo ga Egypt ne bayan da aka kara lokaci a wasan, inda dan wasan Egypt Mahmud Trezeguet ya ci a minti na 100.

A karshen karin lokacin da aka yi, Salah ya kusa kara kwallo ta uku bayan da ta kubcewa 'yan Morocco amma masu tsaron baya sun dakile harin.

Yanzu Egypt za ta kara da Kamaru wacce tuni ta shiga zagayen semi-finals bayan doke Gambia.

A gefe guda kuma, Senegal ta fidda Equatorial Guinea a daya wasan zagayen na quarter-finals.

An tashi a wasan ne da ci 3-1.

Dan wasan Senegal Diehiou ne ya fara zura kwallo a minti na 28, sai dan wasan Equatorial Guinea a Buyla ya farke kwallon a minti na 57.

A minti na 68 Kouyate na kasar Senegal ya kara kwallo ta biyu sai Sarr ya kara wata kwallo ta uku a minti na 79.