Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta nahiyar Afrika (CAF) ta soke karawar zagaye na 2 na neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika (AFCON) a rukunin “d” tsakanin tawagar “Super Eagles” ta Najeriya da takwararta ta kasar Libya “Mediterranean Knight”.
CAF ta wallafa sabon jadawalin gasar a shafinta na X a yau Talata, sai dai, bai hada dana karawar Najeriya da kasar Libya ba.
Tunda fari an tsara cewar karawar zata gudana a kasar Libya da misalin karfe 8 na yammacin yau Talata bayan da zagayen farko ya gudana a filin wasa na Godswill Akpabio, dake birnin Uyo a Juma’ar data gabata.
Tawagar Super Eagles ta lallasa Mediterranean Knight da ci daya mai ban haushi a daf da tashi daga karawar.
Sai dai, takaddama ta dabaibaye zagaye na 2 bayan da ‘yan wasan Super Eagles da masu kula da kungiyar suka bada labarin taskun da suka shiga na tsawon sa’o’i 14 a filin saukar jiragen saman Libya abin da ya tilasta musu dawowa gida.