Wannan shine karo na tara cikin karawa 10 da Masar ta doke Ivory Coast a gasar cin kofin nahiyar Afirka. Fitaccen dan wasa Masar Mohamed Salah ne ya zura ƙwallon ƙarshe, da ya bai wa ƙasanshi damar zuwa zagaye na gaba a bugun daga kai sai mai tsaron gida. Karo na uku kenan da "Giwayen Ivory Coast" suke rashin nasara a bugun fanariti da Masar, bayan wasan karshe na 2006 da kuma na kusa da na karshe a 1998.
Wasan da aka yi tsakanin Mali da Equatorial Guinea shi ma ya kasance cikin shakku. Har ƙarshen lokacin ƙa'ida, ƙasashen biyu suna kunnen doki 0-0. A ƙarshe Équatorial Guinea ta yi nasara a bugun fenariti (6 da 5).
Da haka ne Equatorial Guinea za ta fafata da Senegal a wasan kwata fainal ranar Lahadi mai zuwa. A yayin da Masar kuma zata kara da Morocco. Dukan su a Yaounde.
Kafin wa'annan wasani, za'a kara ranar Asabar a Garoua tsakanin Burkina Faso da Tunisiya. Haka kuma Kamaru mai saukan baƙi za ta fafata da Gambiya a birnin Douala.
Za a buga wasan kusa da na karshe ne a ranakun 2 da 3 ga watan Fabrairu, inda za a yi wasan karshe kuma a ranar 6 ga watan Fabrairu.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mohamed Ladan:
Your browser doesn’t support HTML5