Tun farko a jam’iyar APC sai da aka shafe sa’o’i wakilai wato delegates da yan jarida suka yi ta jira har zuwa cikin dare domin fara gudanar da zaben.
To sai dai kuma kafin fara tantance wakilan ne sai ga sanarwa daga Mallam Nuhu Ribadu, daya daga cikin ‘yan takarar na cewa ya janye daga zaben, bisa zargin cewa ba a tsara zaben bisa turba ba, tunda tun farko sun bukaci ayi yar tinke wato kato bayan kato, to amma aka ki.
Haka kuma Nuhu Ribadun ya musanta rade radin da ake yi na cewa ya marawa daya daga cikin ‘yan takara biyu da suka rage wato Dr Mahmud Halilu Ahmad dake zama kanin matar shugaban kasa da kuma gwamnan jihar Sanata Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla.
Kamar dai jam’iyyar APC, itama PDP an kai ruwa rana kuma har uku daga cikin ‘yan takara bakwai suka fice daga zaben bisa zargin rashin adalci, ‘yan takarar da suka hada da tsohon mataimakin gwamnan jihar Hon. Sa’ad MC Tahir da Dr Umar Ardo da kuma wani na kusa da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, wato Adamu Modibbo.
To sai dai yayin da wasu ke kuka, shugabanin jam’iyyar PDP a jihar na yabawa da yadda lamurra suka gudana. Hon. Abdullahi Adamu Prembe, tsohon kwamishinan yada labaru shine sakataren jam’iyar PDP a jihar Adamawan.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ana can ana kai gwauro da mari a jam’iyyun biyu, inda a APC ake fafatawa a tsakanin ‘yan takara biyu wato a tsakanin Bindow Jibrilla, gwamnan jihar da kuma Dr Mahmud Halilu Ahmad da akewa lakabi da Modi, yayin da a PDP kuwa a tsakanin tsohon mukaddashin gwamnan jihar ne Ahmadu Fintiri wanda ya tsige Murtala Nyako, da Ambassada Jamil Zubairu sai Barista Aliyu Ahmad.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5