Hare-haren kunar bakin wake sai karuwa su keyi a jihar ta Adamawa dalili ke nan da aka kira taron masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro dake jihar.
Gwamnati ce ta kira taron wanda ya kunshi shugabannin hukumomin tsaro da na al'umma saboda lalubo bakin zaren dakile hare-haren.
A wurin taron an fadakar da shugabannin al'umma akan matakan da ya kamata a dauka domin shawo kan matsalar tsaro a jihar.
Alhaji Ahmed Tanko Ningi daraktan hukumar tsaro ta farin kaya a jihar da ake kira SSS yana cikin wadanda suka gabatar da jawabi a wajen taron. Yace kowa mai tsaron kansa ne saboda haka a tashi a kiyaye.
Shi ma gwamnan jihar Sanata Muhammad Bindo Umaru Jibrilla yace nan zuwa makonni biyu jihar zata karbi bakuncin duk manyan jami'an tsaro na kasar da zasu yi babban taro kan harkokin tsaro.
Gwamnan ya roki al'ummar jihar su dinga sa ido akan abubuwan dake kai komo. Yace kowa ya mayarda hankali da inda yake. Kowa mai tsaron kansa ne.
Banda shugabannin addini da na al'umma kungiyoyin dake tallafawa jami'an tsaro a yaki da 'yan ta'adan Boko Haram, wato maharba da 'yansintiri da 'yanbanga da 'yan kato da gora ko Civilian JTF sun kasance wurin taron.
Alhaji Bako Ali Kurna kwamandan Civilian JTF yace zasu cigaba da bada nasu gudummawa amma ya bayyana matsalar da suke fuskanta na rashin samun tallafi daga gwamnatin jihar. Ya kira a kara tsananta bincike a duka mashigan garin.Ya kira gwamnati ta kula dasu.Suna da mata da yara amma gwamnati ba barsu kara zube.
A wurin taron kwamandan sojojin dake Yola ya mika sunayen 'yan Boko Haram da gwamnati ke nema kaman ruwa a jallo. Ya kira a sanarda jami'an tsaro da zara an san inda wani daga cikinsu yake kafin ya aikata barna.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5