WASHINGTON, DC —
Mako daya bayan da bangarorin siyasa a jamhuriyar Nijar suka bada sanarwar amincewa da shirin kafa wani kwamiti, da nufin warware takaddamar dake tsakaninsu.
Akan tsare-tsaren zabubukan 2020 da 2021, kungiyoyin fararen hula sun koka akan abinda suka kira rashin adalci, da aka nuna wajen rabon kujerun wakilcin wannan kwamitin.
Saboda haka shugaban kawancen kungiyoyin ROSEN Alhaji Abdou Maman Lokoko, a zantawarsa da wakilin muryar Amurka Souley Moumouni Barma ya yi kira game da gyara.
Ya kara da cewa dole ne 'yan kasa su samu fahimta, su kuma kama kansu, domin a samu kwanciyar hankali, sannan ya kamata a samu adalci daga bangare gwamnatin kasa.
Ga rahoto cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5