ABUJA, NIGERIA - Membobin jam'iyar sun yi kira akan a bari duk masu son karawa a zaben na watan Mayun su gwada sa’ar su muddin suna son jam’iyyar ta yi nasara a babban zaben shekarar 2023 inda wasu ke ganin akasin haka.
Kiraye-kiraye ga shugabannin jam’iyyar APC mai mulkin su kwatanta adalci ya fara kunno kai ne a daidai lokacin da rahotannin ke nuni da cewa mambobin tsagin jam’iyyar a kusan jihohi 12 sun fara sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP da ma jam’iyyar SDP don samun gurbi a neman takara, duk da cewa ana daf da gudanar da zaben fidda gwaninta a watan Mayun mai zuwa, lamarin da ya fara rikitar da manyan jam’iyyun biyu.
Duk da cewa batun sauya sheka zuwa wasu jam’iyyu daf da lokutan babban zabe ba sabon abu bane a Najeriya masana na ganin cewa kamata ya yi a samo mafita ga sauya sheka ba tare da gamsassun dalilai ba.
Ku Duba Wannan Ma Gwamnoni A Najeriya Na Kara Juya Akalar Siyasar 2023Alhaji AbdulRahman Buba Kwacham shugaban kungiyar matasan arewa maso gabas kuma dan takarar sanatan Adamawa ta Arewa a jam’iyyar APC, yace dauki daura da shugabanni jam’iyyar ke yi bai dace ba.
A halin yanzu dai, akwai rudani a tsakanin shugabannin manyan jam’iyyun siyasar Najeriyar biyu, wato APC mai mulki da kuma jam’iyyar adawa ta PDP, game da rashin jituwar da ke tattare da yadda ‘yan takararsu na shugaban kasa za su fito takara a zaben 2023 sakamakon yawan su.
Abun jira a gani shi ne yadda manyan jam’iyyun biyu zasu samo bakin zare a game da rudanin fidda gwanayensu.
Saurari rahoto cikin sauti daga Halima Abdulrauf:
Your browser doesn’t support HTML5