Adadin Wadanda Suka Mutu Sakamakon Girgizar Kasa A Albania Ya Karu

Albania Earthquake

Yawan wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasa mafi karfi da ta faru a kasar Albania a cikin fiye da shekaru 30 ya karu zuwa akalla 30, a yayin da kasar take zaman makoki na kwana 1.

Minister tsaron kasar Olta Xhacha, muryar ta na rawa, ta karanta sunayen wadanda lamarin ya rutsa da su.

Daga cikin wadanda suka muta da suka hada har da yara, akwai akalla mutane 14 a birni Durres da ke gabar teku, sai kuma wasu akalla 15 a Thumane, da kuma akalla daya a Kurbin.

Jami’ai sun ce adadin wadanda suka mutu din na iya karuwa, yayin da har yanzu ba’a san inda wasu da dama suke ba. An kuma kai wasu da dama da suka ji rauni a asibiti.

Gwamnati ta kafa dokar ta baci a yankunan da lamarin ya fi shafa, a daidai sa’adda ma’aikatan ceto ke ci gaba da aikin tono mutane daga baraguzai.

An kuma tura tawagogin ma’aikatan ceto da kwararru daga makwabtan kasashen Kosovo da Italiya da kuma Girka.

Hukumar kasashen turai ta wallafa a shafinta na twitter, cewa tana tare da Albania, “a wannan mummunan yanayi da take ciki sakamakon girgizar kasa”.