Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lam Tace Zasu Amince Da Sakamakon Zaben Kananan Hukumomi


Shugaban hong Kong, Carrie Lam
Shugaban hong Kong, Carrie Lam

Shugabar Yankin Hong Kong ta ce zata mutunta sakamakon zaben kananan hukumomi wanda ‘yan takarar masu rajin kare Demokradiyya suka yi gagarumar nasara kuma tace wannan zai kawo sauyi sosai.

Shugabar da take dasawa da Beijing, Carrie Lam ta fitar da wata sanarwa jiya Litinin tana cewa gwamnatinta za ta saurari ra’yoyin mambobin jama’a bayan zaben ranar Lahadi da akaga fitowar masu jefa kuri’a da ba’a taba gani ba wanda wani koma baya ne ga Beijing.

“Kadan daga ciki ya nuna cewa sakamakon ya nuna rashin amincewa da irin halin da ake ciki da kuma matsalar da ta dade a cikin al’umma, a cewar Lam.

A cikin sanarwarta ta tace gwamnati za ta saurari ra’yoyin mambobin jama’a da kuma daukansu da muhimmanci.

Sai dai a lokaci zaben na ranar Lahadi, ‘yan takarar 'yan adawa sun lashe kusan kashi 90 na kujerun da suka yi takara, a cewar kafar yada labara ta RTHK. Masu rajin kare demokradiyya yanzu haka suna da iko da kananan hukumomi 17 daga ciki 18, bayan da abaya basu da ko daya.

Zaben wani babban koma bayane ga masu goyon bayan China cewa ta mamaye siyasar Yankin Hong Kong, kuma wannan wata sabuwar hujja ce na cigaba da samun goyon bayan jama’a na shafe watanni biyar da masu rajin kare demokradiyya suka fara da ya cigaba da zama wata annoba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG