Shugabar Hong Kong Carrie Lam, yau dinnan Talata, ta ce sakamakon zaben kananan hukumomi wanda 'yan adawa suka lashe kusan kashi 90 cikin dari na kujerun da aka yi takararsu, na iya zama wata alama ta rashin farinciki da gwamnatinta, da kuma yadda ta bullo ma zanga-zangar rajin dimokaradiyya.
Lam ta ce masu jefa kuri’ar sun nuna yadda su ke ji game da “shugabanci mara inganci,” kuma ta sake maimaita kiran da ta yi na kawo karshen zanga-zangar tashin hankali. Ta kuma sake nanata alkawarin da ta yi a baya na gudanar da tattaunawar a bainar jama'a da zummar warware matsalolin da su ka haddasa zanga-zangar, yayin da ta kasa takamaiman tayi na cgundumomiimma jituwar.
Masu kada kuri'a, a ranar Lahadi, sun yi gagarumin hanunka mai sanda ga kasar China, kuma sakamakon ya nuna cewa masu rajin kare demokradiyya za su yi iko da gundumomi 17 daga cikin gundumomi 18, bayan kuwa a baya ko guda ba su mallaka ba.