Adadin Wadanda Suka Mutu a Rushewar Ginin Legas Ya Karu Zuwa 38

Masu ayyukan ceto a Legas (Facebook/LASEMA)

Ya zuwa yanzu, mutum tara aka ceto da ransu, mace daya da maza takwas a cewar hukumomin jihar ta Legas.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta LASEMA a jihar Legas da ke kudu masu yammacin Najeriya ta ce adadin wadanda suka mutu sanadiyyar ruftawar ginin nan na yankin Ikoyi ya kai 38.

A rana Laraba adadin gawar da aka curo a karkashin baraguzan ginin wanda ya rushe a ranar Litinin ya kai 21.

Mutum tara aka ceto da ransu, mace daya da maza takwas a cewar hukumomin jihar ta Legas.

Rahotanni sun yi nuni da cewa iyalai da abokan arzikin wadanda lamarin ya rutsa da su, sun yi dafifi a wajen da ake aikin ceto mutanen inda suke ci gaba da fatan za a same su da rai.

Ginin mai hawa 21 na kan layin Gerrard Road ne, ana kuma kan gina shi ne tare da wasu tagwayen benaye da ke gefensa.

Gwamnatin Legas ta kafa wani kwamiti don gano musabbabin rushewar ginin.

A ranar Laraba Gwamna Babajide Sanwo-Olu da ya ziyarci wajen aikin ya sha alwashin hukunta duk wadanda aka samu da laifi kan sakacin da ya kai ga rushewar ginin.