Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya kai wa jigo a jam’iyyar APC mai mulki Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ziyara a London.
Wata kungiyar da ke goyon bayan Tinubu ce ta wallafa hotunan wadanda suka nuna Sanwo-Olu zaune tare da Tinubu a wani wuri kamar falo.
A ‘yan kwanakin nan an yi ta rade-radin cewa Tinubu na fama da rashin lafiya a London.
Sai dai wata sanarwa da mai taimaka masa a fannin yada labarai Tunde Rahaman ya yi watsi da labaran da ake ta yadawa mafi akasari a shafukan sada zumunta, wadanda suke cewa tsohon gwamnan na Legas na fama da rashin lafiya a London.
“Lafiyar mai girma Asiwaju Bola Tinubu kalau. Ba ya asibiti, sannan ba shi da wata larura ta rashin lafiya da ta zai ta kai shi ga kwanciya a asibiti.” Rahaman ya ce.
Sai dai Rahaman ya tabbatar da cewa, Tinubu ya fita kasar waje yana mai cewa, “ba da jimawa ba zai dawo.”
Kungiyar “Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Support Group Germany,” ce ta wallafa hotunan a ranar Talata.
Jita-jitar da aka yi ta yadawa cewa Tinubu ba shi da lafiya ta samo asali ne bayan da aka gudanar da zabukan kananan hukumomi a Legas da na shugabannin jam’iyyar APC, ba tare da an ga shi a bainar jama’a ba, abin da bai saba yi ba.