Hukumar da ke yaki da yaduwar cututtuka ta NCDC A Najeriya ta ce yawan mutanen da suka kamu da cutar Kyandar Biri a kasar ya karu zuwa 48.
Hukumar ta NCDC ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis a rahotanta na mako na 34.
NCDC na fitar da rahoto a kowane mako kan cutar ta mpox.
“A rahotonmu na mako na 34 (19-25 watan Agusta), an samu sabbin mutum 8 da cutar ta mpox ta harba a jihohi biyar.
“Hakan ya sa adadin ya haura zuwa 48 na mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar.” NCDC ta ce.
A mako na 33, adadin mutanen da suka kamu da cutar 40 ne.
A ranar Talata Amurka ta ba Najeriya allurar rigakafin cutar ta kyandar biri, hakan ya sa ta zama kasa ta farko a nahiyar Afirka da ta samu tallafin rigakafin.
“Allurar rigakain guda 10,000 za a raba su a jihohi biyar domin kare wadanda suke cikin hadarin kamuwar da cutar.
“Hukumar Lafiya ta Duniya WHO na aiki da sauran abokan hulda don ganin an kara fadada raba allurar rigakafin a sassan Afirka.” WHO ta ce.