Adadin Mutanen Da Suka Mutu A Ruftawar Benen Legas Ya Kai 21

Gwamnan Legas Babajide- Sanwo-Olu (Dama) a wajen ayyukan ceto mutane da gini ra rufata a kansu (Facebook/Gwamnatin Legas)

Har ya zuwa yanzu ba a san iya adadin mutanen da ke cikin ginin ba a lokacin da ya fadi amma ana fargabar akwai akalla mutum 50 a c

Gwamnatin jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya ta ce adadin mutanen da suka mutu a rushewar wani bene a yankin Ikoyi ya kai 21.

Rahotanni sun ce jami’an da ke gudanar da ayyukan ceto sun gano karin wasu gawarwaki a ranar Laraba.

Mutum tara aka ceto da ransu a cewar hukumomin jihar.

A ranar Laraba gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya kai ziyara layin na Gerrard Road da lamarin ya auku, inda ya tabbatar da cewa adadin ya kai 21.

Yadda ake gudanar da ayyukan ceto a wurin da gini ya rushe a Legas (Facebook/Gwamnatin Legas)

A ranar Litinin benen mai hawa 21 wanda ake kan ginawa ya rufta da tsakar rana yayin da ma’aikatan da ke ginin suke aiki.

Har ya zuwa yanzu ba a san iya adadin mutanen da ke cikin ginin ba a lokacin da ya fadi amma ana fargabar akwai akalla mutum 50 a ciki.

Gwamnatin jihar Legas ta kafa wani kwamitin don ya bincike musabbabin rushewar ginin.

Jihar Legas na yawan samun hadurran da suka shafi rushewar gine-gine inda a yawan lokuta akan dora laifin akan amfani da kayan gini marasa inganci da kuma kin bin ka’idojin gine-gine.