Iyalan da suka rasa muhallansu na kwana a matsugunai marasa inganci da aka kafa a Beirut da birnin Sidon dake gabar teku. Inda aka kakkame dakunan otel-otel ko kuma farashinsu yafi karfin iyalai da dama, wadanda basu da matsuguni su rika kwana a motocinsu, a dandali koma a gabar teku.
Issa Baydoun ya tsere daga kauyen Shihine dake kudancin Lebanon sa’ilin da hare-haren bama-bamai suka afka masa. Ya iso Beirut cikin jerin gwanon motocin tare da danginsa. inda suka rika kwana a cikin motoci a gefen tituna bayan da suka fahimci cewar dukkanin wuraren kwana sun cika makil.
“Mun sha bakar wahala a hanya kafin mu iso nan,” a cewarsa.
“Mun bar gidajenmu kasancewar Isra’ila na auna fararen hula tare da kai musu hari,” a cewarsa, wannan shi yasa muka baro gidajenmu, domin baiwa ‘ya’yanmu kariya.”
Masu yi mana fatan alheri sun yi mana tayin gidaje ko dakunan da babu kowa a ciki a shafukan sada zumunta, yayin da masu neman lada suka kafa wuraren girke-girke a wani gidan mai da aka daina amfani da shi a wajen birnin Beirut domin dafawa ‘yan gudun hijira abinci.
-AP