Adadin Mutanen Da Guguwar Helene Ta Hallaka A Amurka Na Karuwa

Yadda guguwar ta Helene ta yi kacakaca da wani yankin Florida

Hukumomi na  gaggawar jigilar kayayyaki tare da maido da hanyoyin sadarwa da tituna a Asheville da ke jihar North Carolina da ambaliyar ruwa ta mamaye a ranar Lahadi.

Adadin wadanda suka mutu na karuwa a kudu maso gashin Amurka da rashin isassun kayayyaki masu muhimmanci a kebabbun yankunan da ambaliyar ruwa ta yi Kamari da kuma asarar gidaje da dukiyoyi yayin da mahukaciyar guguwar da aka yi wa lakabi da Helene ta bayyana karara ga jami’ai da suka yi gargadi kan bakar wahalar da za a sha wajen sake gina inda aka samu barna.

Hukumomi na gaggawar jigilar kayayyaki tare da maido da hanyoyin sadarwa da tituna a Asheville da ke jihar North Carolina da ambaliyar ruwa ta mamaye a ranar Lahadi.

Hakan na faruwa ne yayin da mazauna yankin gabar tekun Florida da guguwar ta shafa suka taru domin gudanar da addu’o’i a coci.

Gwamnar jihar North Carolina Roy Cooper ya ce ana sa fargabar adadin wadanda suka mutu na mutum 11 zai karu yayin da masu aikin ceto suka isa yankunan da lamarin ya shafa.

“Mutane da dama suna ta nuna damuwa kan ‘yan uwan da abokai da ba su gani ba, na daga cikin dalilan da suka sa muka dukufa wajen ganin mun maido da hanyoyin sadarwa.” Cooper ya ce.

Mahukaciyar guguwar dauke da ruwan sama kamar da bakin kwarya ta Helene ta bar mutane da dama da muhallansu yayin da kiyasi ya nuna jimullar mutum sama da 60 ne suka mutu.