Katafariyar gobarar dajin da ta kone unguwanni tare da tilastawa dubban mutane barin gidajensu a birnin Los Angeles ta hallaka akalla mutane 10, a cewar hukumomi, a daidai lokacin da askarawan tsaron California ke shirin dakile rashin doka da oda.
Likitan da ke binciken dalilin mutuwar gawa ne ya sanar da haka a yammacin jiya Alhamis.
Gagarumin aikin kashe gobarar ya shiga cikin dare, inda yake samun tallafi daga jiragen saman shelkwafta masu zubda ruwa sannan an dan samu lafawar iska, duk da cewar ana sabbin harshen gobara na cigaba da kunno kai.
Sakamakon samun rahotannin sace-sace, babban jami’in dan sandan lardin Los Angeles Robert Tuna ya ce ana shirin sanya dokar hana fitar dare, kuma askarawan tsaron jihar California na cikin shirin ko ta kwana domin gudanar da sintiri a yankunan da gobarar ta shafa.
Gwamna Gavin Newsom ya ce askarawan wani bangare ne na dubban jami’an da jihar ta tura.