WASHINGTON, D.C —
Adadin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Amurka ya zarta miliyan 5 a jiya Lahadi, adadi mafi yawa a kasashen duniya.
A jiya Lahadi jami’ar Johns Hopkins ta fitar da adadin, ta kuma ce yawan wadanda suka mutu a Amurka ya haura 162,000.
Cibiyar kididdiga ta kiwon lafiya da nazari da ake kira IHME a takaice ta fitar da wata sanarwa da ke hasashen cewa za'a sami mace-mace kusan 300,000 zuwa 1 ga watan Disamba idan Amurkawa basu maida hankali wajan sanya takunkumin rufe hanci da baki akai-akai ba.
A wata sanarwa daraktan cibiyar IHME Dr. Christopher Murray ya ce idan kashi 95 cikin 100 na Amurkawa suka fara sanya takunkumin rufe hanci da baki, sama da rayuka 66,000 zasu tsira.