Adadin Masu Coronavirus A Najeriya Ya Zarta 10,000

A cikin sababbin alkaluman da hukumar dakile cututtuka ta Najeriya, NCDC ta fitar, wasu daruruwan mutane sun sake kamuwa da cutar coronavirus.

A cewar NCDC, mutum 307 ne cutar ta sake harba a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, wanda hakan ya mayar da adadin masu cutar zuwa 10,162 a kasar.

Har yanzu dai jihar Legas ce ke kan gaba wajen yawan masu dauke da cutar, inda yanzu ta sake samun sabbin kamuwa 188. Sai birnin tarayya Abuja da karin mutane 44.

Sauran jihohin sun hada Ogun (19), Kaduna (14), Oyo (12), Bayelsa (9), Gombe (5), Delta (3), Kano (3), Bauchi (2), Imo (2), Niger (2), Rivers (2), sai jihohin Kwara da Plateau dake da guda daya-daya.

A cewar hukumar, a yanzu haka Najeriya na da mutane 10,162 wadanda suka kamu da cutar, yayin da mutane 3,007 suka samu lafiya, sai kuma mutane 287 da suka mutu.