Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Shiga Jayayya Kan Batun Kafa Kungiyar Tsaron Yankin Ibo


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Har yanzu batun kafa kungiyar tsaro ta yanki na kara janyo takaddama tsakanin mutanen kudu maso gabashin Najeriya, tun bayan wani taron da gwamnonin jahohin yankin su ka yi da kungiyar Ohanaeze Ndigbo ranar Lahadin da ta gabata a birnin Inugu, inda gwamnonin su ka bukaci Majalisun Dokokin Jahohin yankin su kirkiro dokokin da za su ba da ikon kada kungiyar tsaro ta yankin.

Tuni dai aka shiga bayar da ra’ayoyi daban daban kan wannan batu. A yayin da wasu ke ganin hakan na iya kara rarraba kawunan ‘yan Najeriya, musamman a mawuyacin lokacin irin wannan, wasu kuwa gani su ke yanayin tsaro a Najeriay na dada tabarbarewa ta yadda bai kamata a ce yankin na kudu maso gabashin Najeriya ya kasa kafa kungiyar tsaro ta yanki ba.

A wani taron da ya gabaci na baya bayan nan, gwamnonin jahohin yankin sun kare matsayin gwamnatin tarayyar Najeriya na kare al’umma ta tsari na bai daya don haka su ka yi hannu riga da kungiyar Ohanaeze Ndigbo wadda ke son a kafa kungiyar tsaro ta yankin kudu maso gabas mai suna ogbunigwe.

Kungiyar Ohanaeze Ndigbo, da Malam Abdullahi Yayandi daga arewacin Najeriya sun bayyana ra’ayoyinsu kan wannan batun.

Ga wakilinmu Alphonsus Okoroigwe da cikakken rahoton:


Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG