Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Sama Da Mutum Miliyan 5.8 Suka Kamu a Duniya


CORONAVIRUS
CORONAVIRUS

Akwai sama da mutum miliyan biyar da dubu dari takwas dauke da COVID-19 a fadin duniya, haka kuma wasu sama da dubu 360 sun mutu sanadiyar cutar.

Wasu kasashe sun sassauta dokokin hana zirga zirga da suka kafa domin dakile yaduwar cutar, yayin da cutar ke kara yaduwa a wasu wurare.

Amurka dai na ci gaba da zama inda cutar tafi kamari. Sama da mutum miliyan daya da dubu 700 ne aka tabbatar da suna dauke da cutar kana kasar Brazil na biye da mutum sama da dubu 380 dauke da cutar.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi kashedi cewa annobar ka iya haddasa mummunar barna da tsananin wahala a fadin duniya, har da tsananin yunwa da gagarumin rashin aikin yi, idan gwamnatoci basu fara daukar matakan kariya yanzu ba.

Manyan kasashen duniya sun sanar da matakan taimakon su saboda suna iyawa, inji Guterres yana fadawa wani taron kolin da shugabannin kasashe duniya 50 suka halarta.

Firai ministan kasar mai tsibirai a kudancin Pacific Voreqe Bainimarama ya bada shawarar cewa za a iya tattauanawa a kan abin da kasashe masu tasowa ke bukata domin su farfado bayan coronavirus.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG