APC tana son gwamnati mai zuwa ta shirya yiwa jama'a ayyukan da zasu kyautata rayuwarsu.
Muryar Amurka ta tambayi daya daga cikin manyan 'yan jam'iyyar ayyukan da gwamnatin APC zata fara yiwa jama'a. Alhaji Salihu Mustapha yace tun suna kemfen shugaban kasa mai jiran gado yace dole a kula da harkar tsaro. Daga batun tsaro sai samarma matasa aiki domin kada su karkata hankulansu zuwa yin ta'adanci.
To saidai gwamnatin dake barin gado tace sai sabuwar gwamnati ta ci bashi kafin ta iya biyan ma'aikata. Shin yaya sabuwar gwamnatin zata tunkari matsalar. Dr Sani Saidu 'Yandaki darakta janar na kungiyar 'yan kasuwa kuma masani akan tattalin arziki yace sabuwar gwamnati ta fitar da batun sani ko sabo. Wanda ya taka dokar kasa shi ma doka ta takashi. Abu na biyu a kafa kwamitin kwararru wadanda suka cancanta a zauna dasu a tsara yadda za'a yi tafiya. Yace idan aka ce za'a cigaba da tafiya kara zube to idan Najeriya ta wargaje ta wargaje ke nan.
Shi ma Dr Jibo Ibrahim jigo a kungiyar kula da dimokradiya da cigaban kasa yace abubuwa da sabuwar gwamnati tace zata sa gabanta, wato harkar tsaro, samarma matasa aiki da rage cin hanci abubuwa ne da kowa ya yadda dasu. Yace amma duk abubuwa ukun nan suna da wahala a samu canji.Idan kuma ba'a canza ba sabuwar gwamnatin ba zata dade a mulki ba.Kowa ya sa wa sabuwar gwamnatin ido da kyautata zaton ba zata kasa ba kamar gwamnatocin da suka shude. Idan ba canji suka yi ba mutane suka fara gani a kasa su ma zasu shiga cikin rikici.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5