Wasannin Olympics da aka yi a ranar Talata a birnin Tokyo na kasar Japan, sun kasance tattare da koma baya a fannoni da dama da aka kara a gasar.
Babban abin al’ajabi da ya girgiza mutane shi ne, kokarin da ‘yar wasan motsa jiki ko “gymnastic” ta Amurka Simone Biles ta yi don ta kara haskaka bajimtarta a wasan, abin da ci tura.
Biles ta fice a cikin wasan baki daya bayan da ta gaza sauka kan kafafunta a lokacin wata dirar mikiya da ta yi a gasar.
Ta dan fice a zaure wasan tare da mai horar da su, kana ta dawo da kafarta daure da magani ta koma cikin abokan wasanta da suke wakiltar Amurka a Olympic.
Kungiyar wasan gymnastic ta Amurka ta fitar da wata sanarwa dake tabbatar da Simone Biles ta fice daga rukunin ‘yan wasan da suka wasan karshe saboda dalilai na rashin lafiya.
Sanarwar ta ce za a rika kula da lafiyarta a kullu yaumin har lokacin da za a tabbatar da lafiyarta domin wasannin gaba.
Wani sabon abin al’ajabi da ya faru shi ne, shahararriyar ‘yar wasan kwallon “tennis” na mata ‘yar kasar Japan Naomi Osaka, wadda ke matsayi na biyu a duniya ta sha cin kaca a hannun ‘yar wasan Jamhuriyar Czech a zagaye na uku.
Osaka da ta dauki kambun zakarun ‘yan wasan na duniya wadda kuma ake kyautata zaton za ta samu zinari wa kasarta ta sha fama sakamakon wasu kura-kurai da ba a gano ba.
Tun da fari a cibiyar ninkaya ta Tokyo, fafatawar da ake zumudin gani a ninkayar mata ta mita 100 tsakanin Lilly King ba-Amurkiyar nan da ta dauki babban kambun wannan wasa a shekarar 2016 a birnin Rio da kuma ‘yar wasan Afrika ta Kudu Schoenmaker bai je yadda ake tunani ba saboda wata ‘yar ninkayar Amurka da take kungiyar daya da Lydia King mai shekaru 17 ta doke su biyun ta samu zinari.
Schoenmaker ‘yar Afrika ta Kudu ta zo ta biyu kana kana King ta zo ta uku.