Abin Damuwa Ne A Ce ‘Yan bindiga Sun Addabi Jihar Shugaban Kasa – PDP

Gwamnonin PDP a wani taro da suka yi kwanan nan (Twitter/ PDP)

A makon da ya gabata gwamna Masari ya yi kira ga dakarun kasar da su tsaurara matakan tsaro a jihar, inda ya ce a kullum sai ‘yan bindiga sun kai hari a kananan hukumomi 10 cikin 34 da ke jihar.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce alama ce ta gazawa a ce ‘yan bindiga sun gagari gwamnatin jihar da shugaban kasa ya fito.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, dauke da sa hannun sakataren yada labaranta na kasa Kola Ologbondiyan, jam’iyyar ta PDP ta yi kira ga Gwamna Aminu Bello Masari ya dena koke-kokensa na cewa ‘yan fashin daji sun dami jihar, a maimakon haka, ya yi abin da ya kamata.

“Ku bi hanyar da jama’a suka bi, wajen fadawa Shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar ta APC cewa sun gaza.” Ologbondiyan ya fadawa Masari.

A makon da ya gabata gwamna Masari ya yi kira ga dakarun kasar da su tsaurara matakan tsaro a jihar, inda ya ce a kullum sai ‘yan bindiga sun kai hari a kananan hukumomi 10 cikin 34 da ke jihar.

“Abin damuwa ne kuma babbar gazawa ce a ce jihar shugaba Buhari ta fada kangin ‘yan bindiga wadanda ke mamaye kanana hukumomi suna kashe mutane, suna yi wa mata fyade tare da gallazawa fararen hula da ba su ji ba, ba su gani ba.” PDP ta ce.

Jam’iyyar ta PDP ta kara da cewa, ba sabon abu ba ne gazawar shugaba Buhari, musamman kan abin da ya shafi tsaro, tattalin arziki da yaki da cin hanci.