Abin Da ‘Yan Najeriya Ke Cewa Kan Cire Harajin Gas, Man Dizel

Tukwanan iskar gas na girki

Masana tattalin arziki irinsu Dakta Isa Abdullahi Kashere na jami’ar tarayya da ke Kashere a jihar Gombe, na ganin cire harajin abu ne me kyau, kuma hakan zai saukaka hauhawar farashi a kasar, idan har gwamnatin ta ajiye kwarya a gurbinta

Gwamnatin kasar ta bayyana cewa matakin cire harajin VAT akan Iskar Gas, Man Dizel da kuma na CNG zai saukaka lamura acikin kasar.

Mista Wale Edun, wanda shi ne Ministan kudi, ya ce wannan sabbin matakai da suka dauka za su rage radadin tsadar rayuwa da al’ummar kasar ke fama da shi.

Edun ya kara da cewa, matakan za su taimaka wajen rage hauhawar farashin kayayyaki, sufuri da dai sauransu.

Sai dai ‘yan Najeriya dai na ganin daukar wannan matakai kadai ba za su kai su gacci ba.

Yakubu Ali Bulkadimka, daya ne daga cikin manyan dilalan albarkatun mai ta IPMAN, ya ce cire harajin VAT da Gwamnati ta yi, ba zai sauko da farashin Man Dizel ko kuma Iskar Gas a kasar ba, idan har ba a dauki mataki akan masu hana ruwa gudu ba.

Sai dai masana tattalin arziki irinsu Dakta Isa Abdullahi Kashere na jami’ar tarayya da ke Kashere a jihar Gombe, na ganin cire harajin VAT da Gwamnati ta yi akan Man Dizel da Iskar Gas, abu ne me kyau, kuma hakan zai saukaka hauhawar farashi a kasar, idan har gwamnatin ta ajiye kwarya a gurbinta.

Saurari cikakken rahoton Rukayya Basha daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

Abin Da ‘Yan Najeriya Ke Cewa Kan Cire Harajin Gas, Man Dizel.mp3