Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsadar Rayuwa: Ba Gudu Ba Ja Da Baya Kan Zanga-Zangar 1 Ga Watan Oktoba


Wasu masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Abuja
Wasu masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Abuja

Masu shirya zanga-zangar 1 ga watan Oktoba a kan tsadar rayuwa a Najeriya sun jaddada aniyar ci gaba da shirinsu duk kuwa da adawar gwamnatin tarayya a kan hakan da kuma gargadin rundunar ‘yan sandan Najeriya.

Wani tsohon dan takarar shugaban kasa kuma dan gwagwarmaya wanda ya kasance daya daga cikin masu shirya zanga-zangar 1 ga watan Oktoban, Omoyele Sowore, ya yi karin haske a kan batun a shafinsa na X a yau Litinin, inda ya jaddada aniyar ci gaba da shirin, sannan yace za ta gudana a ko’ina a fadin Najeriya.

Ya rubuta cewar, “babu gudu babu ja da baya! #babu tsoro a Oktoba”

Zanga-zangar gama-garin za ta gudana a dandalin Eagle Square dake Abuja, a cewar Sowore.

Yayin da yake bayani game da yadda zanga-zangar zata kasance, Sowore yace za ta kasance ta lumana.

“Zanga-zangar zata gudana a ko’ina a fadin Najeriya saboda girman barna da yunwa da rashin tsaro da tsadar rayuwar da gwamnati mai ci ta haddasa ta mamaye ko’ina a fadin kasar nan. Kuma ina kara nanata cewar, zanga-zangar ta lumana ce, kamar yadda aka saba.

A jihar Legas, masu shirya zanga-zangar sun tsara fara maci daga karkashin gadar Ikeja da misalin karfe 7 da rabi na safe.

Kalaman na Sowore na zuwa ne bayan da rundunar ‘yan sandan Najeriya tace ba a sanar da ita game da kowacce irin zanga-zanga ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG