Abin Da ‘Yan Najeriya Ke Cewa Bayan Da CBN Ya Amince A Karbi Tsofaffin Kudi

Karancin Sabbin Kudi Ya Sa ‘Yan Kasuwan Najeriya Karya Farashin Kayayyakin Masarufi  

Sai dai duk da umurnin da babban bankin ya bayar, rahotanni sun ce har yanzu akwai wasu ‘yan Najeriyar da ke dari-darin karbar kudaden.

‘Yan Najeriya na ta bayyana ra’ayoyin mabanbanta, tun bayan da babban bankin kasar na CBN ya ce za a ci gaba da amfani da tsoffin kudin har zuwa 31 ga watan Disambar bana.

A daren jiya Litinin cikin wata sanarwa bankin na CBN dauke da sa hannun kakakin bankin Isa Abdulmumin, bankin ya umarci bankuna da su rika karbar tsoffin kudaden.

Tun bayan da kotun koli ta yanke hukunci kan cewa a ci gaba da amfani da takardun kudaden naira 200, 500 da 1,000, bankin na CBN ya ki cewa uffan.

Hakan ya sa wasu ‘yan Najeriya da dama kin karbar tsoffin kudaden, lamarin da ya kassara harkokin kasuwanci da cinikayya da dama.

Sai dai sanarwar da bankin na CBN ya fitar a baya nan, ta sa ‘yan Najeriya da dama cikin farin ciki inda suka rika bayyana ra’ayoyi mabanbanta.

“Hakika mun yaba da wannan umarnin da babban bankin kasarmu Najeriya CBN ya bayar, domin ci gaba da yin amfani da tsofaffin takardun kudi na naira” In ji Sani Gulle Kampala Malam-Madori a jihar Jigawa.

Sai dai yayin da wasu key aba matakin na CBN, wasu korafi suke yi kan yadda aka wahalar da al’umar kasar

“An gasawa al'umma aya a hannu an kuma dawo da karbar tsoffin kudi haba shugaba Buhari, ka tuna irin soyayyar da talakawa suka nuna maka lokacin yakin neman zabenka” In ji Kawu Mairuwa Bajoga da Comrade Adamu Abubakar Bajoga.

Shehu Adamu Rijau ana shi tsokacin fata yake za a samu wadatuwar kudaden bayan wannan umarni da bankin na CBN ya bayar.

“To tun da CBN ya amince da hukuncin kotun koli muna fata zai sako mana tsofaffin kudin domin mu ci gaba da amfani da su tun da dai babu sababbin, kuma rayuwa ba za ta tafi daidai ba matukar babu kudi a hannun jama'a.”

Sai dai duk da umurnin da babban bankin ya bayar, rahotanni sun ce har yanzu akwai wasu ‘yan Najeriyar da ke dari-darin karbar kudaden.