La'akari da irin kalubalen da al’ummar Najeriya suka tsunduma ciki, biyo bayan samun yanayin karancin sabbin takardun kudi a fadin Kasar, bayan sauya fasalinsu da Babban bankin CBN ya yi.
A yayin da ya rage ‘yan kwanaki a gudanar da zaben shugaban Kasa da na yan majalisun tarayyar Najeriya, zaben da ake ganin zai sha banban da sauran zabukan da aka taba gudanarwa a tarihin kasar.
A kwai yiyuwar yunwa da talauci da kuma matsanancin matsin tattalin arziki da yawancin al’ummar Najeriya ke fuskanta a halin yanzu, su iya yin tasiri a zaben bana, duk kuwa da matakan da ake ganin an dauka wajen yakar dabi'ar siyan kuri'un al’umma a lokutan zabe.
Masanin tattalin arziki a Najeriya, Dakta Isa Abdullahi, ya ce yanayin da ake ciki zai iya yin tasiri ga rashin nasarar zabubbuka da ke tafe.
Najeriya ta jima tana fama da Matsaloli irin na tsaro da tattalin arziki, wadanda kan haifar da cikas a lokutan zabe.
Toh sai dai a wannan karon, lamarin ya rincabe, ganin yadda al’ummar kasar ke kokawa kan yadda sauya takardun kudin Naira ya haifar da dimbin kalubale ta kowanne fanni na rayuwa, ga kuma karancin sabbin takardun Nairar da ake fama da shi a halin yanzu, lamarin da ya haifar da komabaya a harkokin kasuwanci a fadin Kasar.
Harkokin siyasa a kasashe masu tasowa irin Najeriya, wani abun dubawa ne, musamman a lokutan da ake fama da rashin kwanciyar hankali, sai dai a cewar mai sharhi kan sha’anin siyasa a Najeriya, Hon Sa'idu Gombe, yanayin da ake ciki zai taimaka wajen rage siyasar siyan kuri’u
Domin tabbatar da zaman lafiya tare da kaucewa duk wata hatsaniya da ka iya faruwa a babban zaben dake tafe, shugaban kungiyar One Nigeria, Muhammad Saleh Hassan, ya yi kira ga yan’kasar da su yi fito kwansu da kwarkwatansu wajen yin zabe ba tare da la’akari da halin kuncin da ake ciki ba.
Ana sa ran al’ummar Najeriya za su yi ruwa su yi tsaki wajen zabawa kan su shugaba na gari, da zai samawa kasar sassauci tare da ceto al’ummarsa, daga dimbin matsalolin da aka shafe gomman shekaru ana fama a dasu a hannu shugabannin da suka gabata, mussaman wanda zai farfado da tattalin arzikin kasar da ke fuskantar koma baya ga kuma uwa-uba tarin basussukan da suka yi wa kasar katutu.
Domin Karin bayani saurari rahotan Shamsiyya Hamza Ibrahim.