Tsohon Firai Ministan Zimbabwe, Morgan Tsvangirai ya ce duk abin da ya shafi Najeriay zai iya shafar nahiyar Afrika baki daya ganin yadda kasar ke fama da ayyukan masu ta da kayar baya.
Mr. Tsvangirai ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da Muryar Amurka a Washington inda aka tambaye shi yadda ya ke kallon zabukan da Najeriyar ke tunkara a ranar 28 ga watan Maris.
“Duk wani abu da ya faru a Najeriya, ya na da tasiri akan ragowar kasashen nahiyar Afrika baki daya, sai dai abin takaici shi ne kasar na fuskantar kalubalen samar da tsaro na mayakan sa-kai.” In ji shi.
Game da zabukan, Mr Tsvangirai ya ce ya na fatan cewa za a yi zabe na gari, musamman sai dai ya jaddada matsalar tsaro a matsayin babban kalubale.
Morgan Tsvangirai mai shekaru 63, shi ne babban jagoran ‘yan adawa da ke kalubalantar shugaba Robert Mugabe a Zimbabwe.
Ya taba rike mukamin Firai Minista daga shekara ta 2009 zuwa shekara ta 2013, kuma shi ne shugaban jam’iyar Movement for Democratic Change, wato jam’iyar da ke kokarin samar da canji ta fuskar dimokradiya.
Your browser doesn’t support HTML5