Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ta yi tir da harin da aka kai kan ayarin motocin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar a Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.
Rahotanni sun yi nuni da cewa, a ranar Laraba aka kai hari akan ayarin motocin na Atiku, wanda ya je jihar ta Borno domin gudanar da gangamin yakin neman zabensa.
Wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar a ranar Laraba, dauke da sa hannun sakataren yada labaranta, Debo Ologunagba, ta dora alhakin harin akan “‘yan bangar siyasa da jam’iyyar APC ta dauki nauyin su.”
“Jami’yyarmu ta samu bayanai kan yadda wasu shugabannin APC suka tura ‘yan daba da zimmar tayar da tarzoma a Maiduguri, su kuma hana PDP gudanar da gangamin yakin neman zabenta a jihar.” Sanarwar ta ce.
Kokarin jin ta bakin bangaren jam’iyyar APC wacce ke mulkin jihar ta Borno ya ci tura.
A cewar Ologunagba, magoya bayan jam'iyyar akalla 70 ne suka jikkata a harin, lamarin da ya kai ga kwantar da wasu a asibiti.
Rahotanni sun yi nuni da cewa, an far wa ayarin motocin na Atiku ne jim kadan bayan ya baro fadar Mai Martaba Shehun Borno kan hanyarsa ta zuwa Ramat Square da aka yi gangamin yakin neman zaben.
Atiku ya je jihar Bornon ne tare da abokin takararsa Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta, da gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, da tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido da sauransu.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce an kama mutum guda da ake zargi da hannu a lamarin kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.