Abin Da Masana Ke Cewa Kan Shirin Gyara Halin Tubabbun Mayakan Boko Haram

Tsohon hoto: Wasu tsofaffin mayan Boko Haram da aka sauyawa hali a Jamhuriyar Nijar

Rikicin na Boko Haram ya halaka dubun dubatar mutane ya kuma fantsama har zuwa makwabtan kasashe irinsu Nijar, Chadi da Kamaru.

Hukumomi a Najeriya sun ce shirin nan na gyara halin mayakan Boko Haram da suka mika wuya, na taimakawa wajen karya lagwan kungiyar.

Kalaman hukumomin na zuwa ne yayin da aka yi bikin yaye tsoffafin ‘yan kungiyar ta Boko Haram su kusan 600 a makon da ya gabata.

Sai dai kwararru na cewa, akwai bukatar su ma al’umomin da suka fuskanci hare-haren mayakan a sama musu wani shiri makamancin wannan kamar yadda za ku ji a rahoton Timothy Obiezu, wanda Mahmud Lalo ya fassara.

Akalla tsoffin mayakan Boko Haram da suka mika wuya 590 ne suka yi rantsuwar yin mubaya ga hukumomin Najeriya, a wani bikin yaye su da aka yi, bayan da aka kwashe wani tsawon lokaci ana horar da su kan hanyoyi sauya musu tsattsaurar akida da kuma yadda za su koma rayuwarsu irin ta da a cikin al’uma.

Matasa Tsoffin 'Yan Boko Haram A Nijar

Wannan biki ya wakana ne a karshen makon da ya gabata a jihar Gombe da ke arewacin Najeriya.

Wannan rukunin tsoffin mayakan kungiyar na baya-baya nan da suka ajiye makamai tare da mika wuya sun samu horo a fannon da dama da suka hada da mayar da su hayyacinsu da sauya musu tunanin karkashin shirin na gyara halin da ake wa lakabi da Operation Safe Corridor.

A watan Yulin shekarar 2016 hukumomin Najeriya suka kaddamar da wannan shiri da zimmar cirewa tsoffin mayakan kungiyar mummunar akidar da runguma a da.

“Bisa ga irin horo da suka samu, yanzu wadannan mutane sun za ma nagari, fiye da yadda lokacin da suka zo wannan sansani, kuma sun samu kwarewar da za a iya yaye su, su kuma koma cikin al’uma.” In ji Uche Nnabuihe shi ne jagorar wannan shiri.

Hukumomi sun ce uku daga cikin mutanen da aka yaye daga Nijar da Chadi suka fito, yayin da sauran kuma ‘yan Najeriya ne daga jihohin Borno, Adamawa, Yobe, Zamfara, Neja da Nasarawa.

A lokacin da ake bikin yaye su, tsoffin mayakan sun nuna nadama tare da neman afuwa da yin alkawarin rungumar zaman lafiya a yankunansu da za su koma.

ya ce shirin zai taimaka amma akwai bukatar a yi taka-tsa-tsan.

“Tuba wani abu ne da ke zuciya, wani zai iya ce maka ya tuba saboda wani yanayi da ya tsinci kansa a ciki. Gaskiya, wannan shiri ne mai sarkakiya, shin ina tasirinsa yake, shin ya hana kungiyar diban sabbin mayaka? Mai fashin baki kan sha’anin tsaro Senator Iroegbu ya ce.

Wasu daga cikin mayakan Boko Haram da suka mika wuya

Sai dai hukumomi sun ce akwai dubban tsoffin mayakn da aka yaye karkashin wannan shiri tun daga shekarar 2019, kuma sun zama mutane nagari a cikin al’uma.

A shekarar 2021 hukumomi a jihar Borno, suka yi kiran da a sake yi wa shirin garambawul, suna masu cewa akwai yiwuwar tsoffin mayakan su zama masu kwasar bayanai suna aikawa kungiyar, daga baya ma har su komawa ruwa.

A yankunan da mayakan suka fito ma akan nuna shakku kan wannan shiri na sauya halin tsoffin mayakan na Boko Haram da suka tuba.

Vivian Bellonwu, ita ce shugabar kungiyar Social Action Nigeria mai tallafawa al’umomin Najeriya.

“Ga dukkan alamu, ayyukan gyara halin ya ta’allaka ne akan ‘yan tawayen, bayan kuma su ma al’umomin da abin ya kare a kansu sun galabaita tare da shiga yanayi na dimuwa. Kuma su ma akwai bukatar a sama musu wani shiri da zai dawo da su cikin hayyacinsu, su ma a warkar da su daga mummunan al’amuran da suka gani. Amma ni ban ga an yi wani abu makamancin hakan ba.” In ji Bellonwu.

“Wadannan al’umomi ne da aka ta garkuwa da su. An yi wa matansu fyade. Wasu yara suna kallo aka kashe iyayensu. Irin wannan al’amari kan zauna zakutan mutane na wani tsawon lokaci. Ta yaya kake tunanin za su manta? Bellonwu ta kara da cewa.

Wasu mayaan Boko Haram/ISWAP da suka mika wuya da makamai (Facebook/Dakarun Najeriya)

Tun daga shekarar 2009, kungiyar ta Boko Haram take kai hare-hare, inda take ikirarin kokarin kafa daular Musulunci a arewacin Najeriya

Rikicin na Boko Haram ya halaka dubun dubatar mutane ya kuma fantsama har zuwa makwabtan kasashe irinsu Nijar, Chadi da Kamaru.

A ranar Lahadin da ta gabata, hukumomin tsaro suka ce mayakan Boko Haram dubu 51 ne suka da iyalansu suka mika wuya, tsakanin watan Yulin 2021 da watan Mayun bara.

Your browser doesn’t support HTML5

Abin Da Masana Ke Cewa Kan Shirin Gyara Halin Tubabbun Mayakan Boko Haram