Abin Da Manjo Hamza Al-Mustapha Ya Ce Kan Kudaden Da Ake Zargi Abacha Ya Boye

Janar Sani Abacha.

A hira da Muryar Amurka a Kano, Manjo Almustapha, ya ce kokarin batawa Abacha suna ne ya sa ake ci gaba da alakanta shi da wadancan kudade shekaru 22 bayan rasuwarsa.

Tsohon mai tsaron lafiyar shugaban mulkin soja Najeriya marigayi Janar Sani Abacha, kuma dan takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar Jam'iyyar Action Alliance, a zaben shekara ta 2023 da ke tafe, ya ce tsoron da aka cusa a zukatan wasu daga cikin 'yan kasuwa da attajirai a Najeriya ne ya sanya suka gaza yin magana dangane da batun kudaden da ake cewa tsohon shugaba Abacha ya boye a bankunan kasashen duniya.

Cikin wata hira ta musamman da ya yi da Muryar Amurka, Manjo Hamza Almustapha ya ce kudade da ake dangantawa da marigayi Abacha, kokari ne na bata masa suna.

Ku Duba Wannan Ma Jam’iyyar PDP Na Gudanar Da Zaben Fidda Gwani Na ‘Yan Takarar Gwamnonin Jihohin Najeriya

Al Mustapha ya kafa hujja da cewa, da a ce kudaden na Abacha ne, da an ga sa hannunsa a bankunan da aka ajiye kudaden.

Saurari yadda hirar ta su ta kaya da wakilin Muryar Amurka, Mahmud Ibrahim Kwari:

Your browser doesn’t support HTML5

Tsoro Ne Yasa Attajirai, ‘Yan Kasuwa Basa Batun Kudaden Da Aka Ce Abacha Ya Boye-Manjo Hamza Almustafa.mp3