Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar NNPP a Najeriya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya kammala ziyarar da ya kai Maiduguri, babban birnin jihar Borno a karshen makon nan.
Yayin ziyarar ta kwana biyu, Kwankwaso ya kaddamar da ofishin jam’iyyarsu ta NNPP da ke birnin Shehun zagaye da dandazon magoya jam’iyyar.
Kaddamar da ofishin jam’iyyar na zuwa ne, kwanaki uku bayan da rahotanni suka nuna cewa ‘yan sanda a jihar sun rufe ofishin na NNPP a garin na Maiduguri.
Bayanai sun yi nuni da cewa, hukumar da ke bunkasa birnin na Maiduguri ce ta sa aka rufe ofishin a ranar Alhamis bisa zargin karya dokar tsarin birnin.
Sai dai Gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum ya ba da umarnin a bude ofishin ba da bata lokaci ba.
Yayin da yake bude ofishin a karshen makon nan, Kwankwaso ya fadawa dandazon magoya bayan jam’iyyar cewa, idan suka kafa gwamnati, za su mayar da hankali kan batutuwa da dama da za su amfani da al’uma.
“Babban aiki ne a gabanmu gaba ki daya, ya kasance duka arziki kowa ya amfana, ya kasance an samu tsaro, kowa a ba shi jari, kowa a bude masa makaranta, a bude asibitoci.
“Ko mutanen da na gani, da idona daga airport zuwa gurin nan, in Allah ya yarda NNPP ta ci zabe dari bisa dari a jihar nan ta mu.” Tsohon gwamnan jihar Kano, Kwankwao ya ce.
“A ci gaba da addu’a, halin da kasar nan take ciki, musamman ma wannan bangare na Najeriya, abin takaici ne.” Kwankwaso ya kara da cewa.
Borno, jiha ce da dan takarar mataimakin shugaban kasa karkashin jam’iyya mai mulki ta APC Kashim Shettima ya fito, kuma tana karkashin mulkin jam’iyyar at APC ne.
Jihar har ila yau ta kasance cibiyar rikicin Boko Haram wanda ya faro tun daga shekarar 2009, ko da yake, lamarin ya lafa.
Saurari cikakken rahoton Haruna Dauda Biu:
Your browser doesn’t support HTML5