An kafa dokar hana fitar ne a garin Aba daga karfe shida na safe zuwa karfe shida na yamma. Haka kuma dokar zata kwashe kwanaki uku tana aiki.
Sai dai kuma duk da dokar da gwamnatin Abia ta kafa har yanzu yan arewa na cikin fargaba sakamakon farmakin da aka kai musu. Wanda yayi sanadiyar rayuka da kuma jikkata wasu.
A cewar Alhaji Sallau, shugaban kasuwar Albasa Aba, yanzu haka an kawo musu gawarwakin mutanen da aka kashe guda hudu, haka kuma akwai mutane sun kai arba’in kwance a asibiti.
A jihar Rivers dake yankin Niger Delta ita ma an sami irin wannan farmaki kan al’umomin arewacin Najeriya, sai dai kuma bayanai na tabbatar da cewa an fara samun lafawar lamarin bayan da hukumomi suka dauki matakan da suka kamata.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya dai ta tabbatar da mutuwar mutane uku a arangamar da aka yi a garin Aba na jihar Abia.
Domin karin bayani saurari rahotan Lamido Abubakar.
Your browser doesn’t support HTML5