Tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilan Najeriya Abdulmumuni Jibrin, ya ce alwus din da ya kama daga Naira miliyan goma zuwa ashirin ake damkawa ‘yan majalisar wakilan duk wata.
Can baya ma akan cure kudin kamar Naira miliyan dari biyu a damkawa dan majalisa a shekara, da yayi zargin hakane yasa su shiru kan aringizo a kasafin kudin bana.
Jibirin, wanda majalisar ta dakatar kuma ta garkame ofishinsa yace zai mayarwa majalisa irin wadannan kudaden da aka bashi a baya, kuma yana kalubalantar sauran abokan aikinsa su dari ukku da hamsin da tara su dawo da kudin da ake basu da suka wuce gona da iri.
Da yake maida martini na hannun damar kakakin majalisar, dan majalisar tarayya, Ustaz Yunus Ahmad Abubakar, bai musanta karbar kudin ba sai dai yace sam basu kai Naira miliyan goma ba kuma ana amfani da kudin don gudanar da lamuran aikin majalisar ne.
Babbar kotun Najeriya, zata fara sauraren karar kalubalantar dakatar da Abdulmumini Jibrin, ranar ashirin da daya ga watan nan. Hukiumar EFCC, na ci gaba da binciken zargin aringizon a majalisar wakilai.
Your browser doesn’t support HTML5