Abdulmumin Jibrin Ya Bukaci Shugaba Buhari Ya Yi Murabus

Rubutun da dan majalisar wakilan Najeriya, Abdulmumin Jibrin yayi a shafinsa na Twitter, inda ya bukaci shugaban kasa Muhammdu Buhari ya sauka daga mulki domin a nasa ra’ayin shugaban ya kasa samar da sauyin da ake bukata na haddasa martani da mutane ke ganin ya yi azarbabi.

A halin da ake ciki, Jibrin, na ci gaba da zaman dakatarwa na kwanaki Dari da Tamanin da majalisa ta debar masa, duk da ya kai kara kotu, har yanzu bai dena sukar ‘yan majalisar wakilai da yin aringizo a kasafin kudi ba.

Bayan ganawarsu da shugaba Buhari kan kasafin kudi da mu’amular sashin zartaswa na majalisa, kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, ya masa tambayar da ta kasance tamkar hannunka mai sanda kan irin wannan caccakar.

Ya’u kaca, daya daga cikin bangaren magoya bayana shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya mayar da martanin cewa a matsayin Abdulmumin Jibrin, na dan siyasa, ya bar Jaki ne yana dukan Taiki, domin bashi da hurumin da zai yi wannan Magana. Ya kara da cewa korar da aka yi masa daga kwamiti na kasafin kudi ce tasa yake ta wadannan maganganu.

Jibrin, ya bayyana cewa baya tsammanin wani sassauci akan abinda ya zayyana a matsayin gwagwarmayar gyaran majalisa da yake kokarin yi kamar yadda ya bayyanawa wakilin sashin Hausa na muryar Amurka, Nasiru Adamu El-Hikaya.

Ga rahoton da Nasiru Adamu El-Hikaya ya aiko mana.

Your browser doesn’t support HTML5

Abdulmumin Jibrin Ya Bukaci Shugaba Buhari Ya Yi Murabus