Darakta kuma furodusa a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Abdul Amart Mai Kwashewa, ya saya wa iyalan marigayi Aminu S. Bono muhalli.
A ranar 20 ga watan Nuwamba Allah ya yi wa darakta Bono rasuwa a Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Mutuwarsa ta girgiza mutanen da ke ciki da wajen masana’antar ta Kannywood duba da cewa ta farar daya ce.
“Mutum ne (Bono) da ya kamata tsakani da Allah mu tsaya mai, mu tabbatar ‘ya’yansa sun taso cikin aminci, shi ne karshen kauna da za mu iya nuna mai.” Mai kwashewa ya fada bayan addu’ar bakwai a wata hira da ya yi da Nagudu TV.
Da yake fadan abin da ya zaburar da shi ya yi wannan aiki, Mai Kwashewa wanda shi ne shugaban kamfanin Abnur Entertainment, ya ce suna tunanin yadda za su taimakawa iyalan Bono ne sai ya samu labarin cewa kudin hayansa zai kare a wannan wata.
“A shawarce, sai na ce a nemo gida a kusa da gidan iyayensa, Allah kuma cikin ikonsa, ban shirya ba, Allah ya taimake ni na yi wannan abun.” In ji Mai Kwashewa wanda shi ne furodusan fim mai dogon zangon na "Manyan Mata."
Mai Kwashewa na daya daga cikin na hannun daman marigayi Bono, wanda ya yi aiki karkashin kamfanin Abdul Amart tun kafin ya yi suna.
“Mutum ne da ya taimake ni a harkar sana’ata, mene ne za ka masa, ill a ce ka rike masa iyalensa. In Allah ya yarda ba za su wulakanta ba saboda kyawawan halayensa.” Mai Kwashe wa ya ce.
A ranar da ya rasu, fitacciyar jaruma a masana'antar ta Kannywood Aisha Humaira, ta ce da dauki nauyin sauke masa dukkan basussukan da ake bin sa.
Rasuwar Bono na zuwa ne sama da shekara guda bayan mutuwar darektan fim din “Izzar So” mai dogon zango, Nura Mustapha Waye, wanda shi ma Allah ya yi wa cika wa ta irin makamancin wannan yanayi na mutuwar farar daya.