“Kalaman na zababben Gwamna riga malama masallaci ne saboda idan kana ba da umurni kan abin da ya shafi gwamnati kuma gwamna mai ci bai kammala wa’adinsa ba, hakan zai iya janyo rudani.”
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga zababben gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, da ya daina yin riga malam masallaci domin har yanzu shi ne gwamnan jihar.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Malam Muhammad Garba, Ganduje ya ce ba daidai ba ne Yusuf ya rika ba da umurni kan al’amuran da suka shafi gwamnati.
“Kalaman na zababben Gwamna, riga malama masallaci ne saboda idan kana ba da umurni kan abin da ya shafi gwamnati kuma gwamna mai ci bai kammala wa’adinsa ba, hakan zai iya janyo rudani.” Sanarwar ta ce.
Rahotanni sun ruwaito Yusuf wanda ya lashe zaben gwamna da aka kammala karkashin jam’iyyar NNPP yana cewa, mutane su dain gine-gine a filayen da suka kasance mallakin gwamnati ne.
“Har sai lokacin da ya karbi rantsuwa ya shiga ofis a ranar 29 ga watan Mayu, zai ci gaba da zama a matsayin zababben gwamna ne kuma ba shi da karfin ikon Gwamna.
“Abin da zai iya yi kawai shi ne, idan ya shiga ofis zai iya sauya wasu tsare-tsare da wanda ya gabata ya aiwatar.” In ji Garba.
Yusuf ya kada da dan takarar jam'iyyar APC Yusuf Gawuna a zaben na gwamna wanda aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.