Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Lauya Mai Zaman Kansa A Kano Ya Gurfanar Da Gwamnan Jihar Gaban Babbar Kotu


Gwamna Ganduje na jihar Kano, (Instagram/Abdullahi Umar Ganduje)
Gwamna Ganduje na jihar Kano, (Instagram/Abdullahi Umar Ganduje)

Wani lauya mai zaman kansa a Kano ya gurfanar da gwamnan Kano gaban babbar kotun Kano, yana kalubalantar tsarin gwamnatin jihar na haramtawa mutane fita daga karfe 7 zuwa 10 na safiyar ranar Asabar din karshen kowanne wata.

Tun shekarun zamanin mulkin soja ne dai gwamnatin ta kebe wadannan sa’o’i guda uku, inda ake hana zirga zirgar mutane a birni da kewayen Kano domin Jama’a su gudanar da aikin shara da tsaftace muhallin su.

Kamar yadda takardar karar da lauyan Barrister Ibrahim Baba ya gabatarwa kotun ta nuna wadanda ake kara sune gwamnan na Kano da kwamishinan ‘yan sanda na Kano da kwamishinan shari’a kuma Atoni Janar na Kano da kwamishinan Muhalli kana da ma’aikatar muhalli ta Kano.

Barr. Ibrahim Baba wanda ya yi karin haske game da kunshin karar yace hana mutane zirga zirga a cikin wadannan sa’o'i sun tauye hakkin sa a matsayin na dan jihar Kano da sauran mutane mazauna jihar Kano, yana mai cewa matakin ya ci karo da tanade tanaden ‘yancin walwala da kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa ‘yan kasa da kuma daftarin kare hakkin dan adam na nahiyar Afrika.

A cewar Barr Ibrahim Baba, akwai banbanci tsakanin tsaftar muhalli da haramta zirga zirga Jama’a a gari.

Yanzu dai abin jira a gani shine yadda zata kaya a gaban babbar kotun ta Kano.

Saurari cikakkeb rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

XS
SM
MD
LG