A Twitter An Kafe Hotan Sojan Amurka Da Aka Kashe a Nijar

Rundunar Sojan Amurka dake aiki a nahiyar Afirka

Rundunar sojan Amurka na yin bitar wasu hotuna da aka kafe a kafar sada zumunta ta Twitter dake nuna wani sojan Amurka da aka kashe lokacin da aka yi musu kwantan bauna a jamhuriyar Nijar a shekarar da ta gabata.

A jiya Laraba ne rundunar sojin Amurka dake aiki a nahiyar Afirka da ake kira AFRICOM, ta ce tana sane da hotan da aka sa a dandalin Twitter, kuma tana binciken gano sahihancin abin da aka kafen, kuma gano gaskiyar cewa akwai hoton bidiyo hoton.

Rubutun da aka yi na cewa hotan ya fito ne daga wani hotan bidiyo mai tsawon mintoci goma da kungiyar ISIS ta yada a Mali. Haka kuma sanarwar da aka yi ta ‘kara da cewa hotan bidiyon ya nuna sojan Amurka da ya sami rauni da kuma gawarwakin sojoji uku da aka kashe ranar 4 ga watan Oktoba a harin kwantan baunar.

‘Yan bindigar dai sun kai harin ne kusa da kauyen Tongo Tongo, inda suka kashe sojojin Amurka hudu da na Nijar hudu da kuma wani mai fassara ‘dan Najeriya.

Ana sa ran kamalla binciken da ake gudanarwa kan mummuman harin kwantan baunar zuwa karshen watan nan.