Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KENYA: Mata Sun Kalubalanci Kin Basu Dama a Gwamnati


Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta.
Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta.

Daruruwar mata sun yi zanga zanga a Nairobi babban birnin kasar Kenya a jiya Litinin a kan gazawar shugaban kasar wurin baiwa mata kashi talatin cikin dari na mukaman gwamnatinsa kamar yanda kundin tsarin mulkin Kenya ya shata.

Makwanni biyu da suka wuce shugaba Uhuru Kenyata ya aiwatar da garanbawul a majalisar ministocinsa kuma ya zabo wasu mutane tara da zai nadasu akan muhimman mukaman gwamnatinsa. Amma babu mace ko guda a cikin mutane tara da zai nadasu manyan mukaman. Ya kuma yi waje da mata guda biyar dake cikin ministocinsa

A kan wannan dalili ne kungiyoyin fafutuka karkashin jagorancin shugaban cibiyar rajin kare hakkin bil adama da ilimi da wayar da al’umma Wangeci Wachira suka shirya wannan maci zuwa fadar shugaban kasa ta Harambee House suka gabatar da kokensu, a kan bukatar nada mata akalla guda tara mukaman minista

Ana daukar kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 2010 a matsayin nasara ga mata wanda aka kwash lokaci mai tsawo ana tauye musu hakkokinsu a harkar siyasa da kuma hanasu mukamai a hukumomin zartarwar kasar.

Kundin tsarin mulkin ya tanada cewa mata su rike akalla kashi daya cikin uku na kujerun majalisar dokoki da kuma na mukaman gwamnati. Kana kuma a ware wasu kujerun majalisa 47 da mata kadai zasu yi takara a kai.

Duk da haka, ba a aiwatar da tsarin da kundin tsarin mulkin ya tanada na ba mata wadannan guraban. A zaben kasar Kenya na baya bayan nan da aka gudanar a bara, mata 23 kacal ne aka zabesu a kujerun majalisar kasa.

Wasu kungiyoyin kare yancin dan adam guda biyu a Kenya sun shigar da kara a babban kotun kasar suna nema a tilasa gwamnati ta bi tsarin kundin mulkin kasar, ta ba mata mukaman gwamnati. Sai dai kotun bata bada lokacin da zata yanke hukunci a kan wannan kara ba.

Ga Grace Alheri Abdu da fasarar rahoton wakiliyar Muryar Amurka Rael Ombuor a birnin Nairobi.

Zanga Zangar Mata a Kenya-3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG