Kungiyar Fulanin Ghana ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta kawo masu doki domin dakatar da cin zarafin da ta ce gwamnatin kasar na yi wa Fulani tare da kashe shanunsu.
Fitina tsakanin Fulani makiyaya da manoma a jihar Ashanti da gabashin Ghana ya yi munin da har gwamnatin kasar ta kafa wani rukunin aiki na sojoji da 'yan sanda domin dakile matsalar da ta ba umurnin harbe duk shanun da suka hango tare da masu kiwonsu. A cewarsu hakan ya yi sanadiyyar kashe shanu fiye da 500 a cikin garin Agugu da gundumar Shatuwapam Plains.
Ganin yadda cin zarafin ya yi yawa ya sa kungiyar ta Fulani ta kira taron manema labarai ta mika kokenta ga duniya. Shaikh Usman Bari shugaban kungiyar ya bayyana makasudin taron inda ya ce suna son su nunawa duniya gaba daya irin cuta da cin zarafin da ake yi masu a Ghana da zummar samun masalaha.
Wani makiyayi, Alhaji Umar ya ce babu inda zasu juya da shanunsu duk da cewa suna biyan kudin yin kiwo kowace shekara.
Amma Alhaji Alfa cewa ya yi akwai son rai da nuna bambanci a cikin abubuwan dake faruwa. A cewarsa kiwo na cikin sashin noma amma 'yan jarida sun mayar da lamarin tamkar matsalar baki ne da 'yan kasa.
Shi ko Malam Imrani Ibrahim masanin harkokin duniya ya yi tsokaci akan irin matakan da ake dauka domin samar da mafita. Ya ce tattaunawa da juna ne zai kawar da matsalar kuma yana ganin hadin kai da shugabannin kasar zai kaiga masalaha.
Ridwan Abbas na da karin bayani
Facebook Forum