Daya daga cikin manyan masu baiwa shugaban Amurka shawara akan tattalin arziki Larry Kudlow ya fadawa yan jarida a jiya Laraba cewa shugaba Donald Trump na Amurka zai tsaya akan bakarsa wajen taron kolin kungiyar kasashe masu arzikin masa’antu da ake cewa G7 a takaice, da za’a yi duk da cacakar manufofi harkokin kasuwancin Amurka da kawayen Amurka suka yi ko kuma suke yi.
Mr Kudlow yace galibi akan samu sabanin ra’ayi tsakanin Amurka da sauran kasashe wakilan kungiyar G7. Mr Kudow ya musunta cewa Amurka tana rikici akan harkokin cinnikaya da kawayen ta da kuma China, amma yace Amurka zata dauki duk matakan da suka kamata na kare ma’aikatan Amurka da masana’antunta.
Sakataren tsaron Amurka Jim Mattis a yayinda yake zantawa da yan jaridar a birnin Brussels kasar Belgium a jiya Laraba yace za’a yi garaje ga dami a baiyana rikicin jadawalin kudi fito a zaman rikicin harkokin kasuwanci kuma ya hakake akan cewa Amurka tana da hujjar neman ayi mata adalci a harkokin kasuwanci da kawayen ta.