A wani kiyasi da hukumar lafiya ta Duniya ta fitar ya nuna cewa fiye da mutane miliyan 400, ne ke dauke da cutar a fadin duniya a shekara ta 2014, sabani mutane miliyan 108, dake dauke da cutar a shekarar 1980, wannan na nuna karuwar cutar tun daga shekarar 1980.
A cikin wannaan adadi kimanin mata miliyan 205, ke dauke da cutar, taken ranar a bana ta masu dauke da wannan cuta ya ta’allaka ne akan mata masu dauke da wannan cuta da kuma hanyoyin da za a biyu domin rage daukar cutar.
Masana kiwon lafiya na alakanta wannan cuta, ga kiba da kuma ciye ciyen abinci na zamani da ya zama ruwan dare, a tsakanin al’umar duniya, wani matsala da masu dauke da wannan cutar ke kuka akai shine tsadar magungunan da suke sha domin magance wannan cuta ko kuma rage kaifinsa.
Wani Likitan hada magunguna Salihu Ibrahim, ya ce magungunan da ake amfani dasu akan cutar ciwon sukari, sun kasi kamar kashi biyu inda akwai dangin allura wanda akan koyawa mai cutar yadda zai iya yiwa kansa sannan kuma sai wanda ake sha ta baki, duk wadannan magunguna ana amfani dasu ne domin daidaita sukari dake jikin mutun.
Ya kara da cewa kawo yanzu a dai duniyar kimiyar magani na bature babu magani waraka daga cutar sukari sai dai a samu saukin kada cutar ta kai matsayin da zata yiwa mara lafiya lahani.
A sabili da tsadar magunguna wannan cutar ne yasa masu dauke da wannan cutar kira ga gwamnati da ta taimaka wajen bada tallafi na irin wadannan magunguna kamar yadda ake baiwa masu dauke da cutar HIV AIDS ko kuma CIDA.
Your browser doesn’t support HTML5