Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Jami’an Gwamnatin Borno Sun Kalli Majigi Akan Boko Haram


Irin barnar da kungiyar Boko Haram ta haddasa a jihar Borno
Irin barnar da kungiyar Boko Haram ta haddasa a jihar Borno

A ci gaba da nuna majigin da VOA ta shirya, wasu jami’an gwamnatin jihar Borno, jihar da ta fi kowace jiha a arewa maso gabashin Nigeria, fama da rikicin Boko Haram, sun kalli majigin sun kuma tofa albarkacin bakinsu

Majigin mai taken ‘Tattaki daga Bakar Akida” an nunawa wasu manyan jami’an gwamnatin jihar Borno Litinin.

Manufar majigin itace nuna irin jajircewar da al’ummar Najeriya suka yi, musamman a arewa maso gabashin kasar inda jihar ta Borno ke kan gaban sauran jihohin da suka yi fama da Boko Haram.

Majigin ya haskaka irin matsalolin da aka dinga fuskanta kama daga hare-haren ‘yan kungiyar Boko Haram zuwa kone-konen gidaje da makarantu da kuma irin hukunce hukuncen da kungiyar ke dauka kan jama’a da dai sauransu.

Dr Muhammad Bulama kwamishanan yada labarai da al’adun gargajiya na jihar ya y aba da majigin y ace yana da mahimmanci sosai. Majigin zai tunasar ya kuma fadawa wadanda ma basu san batun Boko Haram abubuwan da suka gudana da kuncin da jihar da sauran arewa maso gabas suka shiga har na tsawon shekaru takwas. Y ace a nasu bangaren zasu taimaka wurin yada majigin domin a samu cikakkiyar fahimta.

Alhaji Baba Kura Abba Jatau shugaban gidan rediyo da talibijan mallakar jihar Borno y ace yanzu zaman lafiya ya dawo Maiduguri amma duk wanda ya kalli majigin ko bai taba jin Boko Haram ba zai san jama’a sun shiga wani mugun hali can baya kuma sun tagayyara. Ya yabawa Muryar Amurka dangane da namijin kokarin da tayi.

Yayinda yake bayyana dalilin shirya majigin Aliyu Mustapha y ace ana son mutane su ga yadda rigingimun Boko Haram suka shafi rayuwar al’ummar yankin arewa maso gabas

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG