Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, ya nuna alhininsa bisa kisan da masu garkuwa da mutane suka yi wa Hanifa ‘yar shekara 5 a Jihar Kanon Najeriya.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Atiku Abubakar, ya kwatanta lamarin a matsayin “mummunan labari.”
“Na samu mummunan labarin kisan gilla ga yarinya Hanifa ƴar shekaru 5, wadda aka kashe bayan kwashe kwanaki 47 a hannun masu garkuwa.
“Wannan dabbanci da rashin imani ne. Na kasa gane yadda mutum mai hankali zai raba yarinya karama da iyayenta tare da kashe ta.” Atiku Abubakar, ya ce cikin sanarwar da ya wallafa.
Ku Duba Wannan Ma APC Za Ta Gudanar Da Babban Taron Ta Na Kasa A Watan GobeAtiku ya kuma miƙa sakon jajensa tare da yin ta'aziyya ga iyalan Hanifa yana mai kira da a bi mata kadinta.
“Ina kira ga mahukunta da su tabbatar (masu garkuwar) sun fuskanci hukunci."
A ranar 4 ga watan Disambar 2021, malamin Hanifa Abdulmalik Tanko ya yi garkuwa da ita inda ya kai ta gidansa ya ajiye ta har tsawon mako biyu kafin daga bisani ya kashe ta.
Kamar yadda ya fadawa jami’an tsaro, malam Tanko ya ce ya yanke shawarar kashe dalibar ta sa ne bayan da ya yi tsammanin cewa an gano shi ne ya sace ta.