A Shirye Muke Mu Fafata Da Kwaddebuwa, Inji Shugaban Kwallon Kafa Ta Najeriya

Dan wasan Najeriya, Victor Osimhen a karawar Najeriya da Equatorial Guinea

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Nigeria Alh. Ibrahim Gusau yace bashi da wani shakku akan wasan da Super Eagle zata kara da mai masaukin baki a gasar cin kofin Afrika da a ke yi yanzu haka a kasar Kwaddebuwa.

A wata zantawa da Muyar Amurka, Alhaji Ibrahim Gusau yace sun yi duk wani shirin da ya kamata domin tunkarar wannan wasa da za a gudanar a ranar 18 ga watan Jana'irun 2024 cikin ikon Allah.

A dangane da wasan da Nigeria ta Buga a baya Alh. Gusau yace suna baiwa 'yan Nigeriar hakuri akan abinda ya faru kuma a yanzu sun dauki mataki kuma hakan ba za ta sake faruwa ba.

Ya kara da cewa suna da kwarin guiwa sosai akan 'yan wasan Nigeria.

Haka zalika, Alh. Gusau yace ba su da wata matsala akan biyan hakkokin 'yan wasan na Super Eagles domin Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da duk wani abu da aka rubuta domin biyan 'yan wasan,

Sai dai ya bukaci 'yan Najeriar su cigaba da yi masu addu'o'i na musamman domin ganin sun dawo da wannan Kofi.

Ga cikakken hirarsa a sauti da wakilin Muryar Amurka, Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

A Shirye Muke Mu Fafata Da Kwaddebuwa, Inji Shugaban Kwallon Kafa Ta Najeriya